Shugaban ƙasar Najeriya Muhammad Buhari ya bayyana cewa ƙin kai yara makaranta a wannan lokaci ya zama babban laifi, wanda ya saɓawa sashi na 18(2) cikin dokar najeriya,na wajabcin bada Ilimi ga yara.

Buhari ya bayyana hakan a taron tattaunawa kan tattalin Arziƙin Najeriya, da gwamnoni 36 na jihohi.
A cewarsa sashi na 2 ya wajabta cewa dole ne a bada ilimi kyauta a ilimin bai ɗaya, da ƙaramar sakandare, a sabo da haka ƙin kai yara makaranta laifi ne.

Ya kuma yi kira ga gwamnoni da su tabbatar sun wadata makarantu da kayan koyo da koyarwa, da kuma tabbatar da cewa an bawa ilimin bai ɗaya kwakkwawan kulawa.
Buhari yace a ɓangarensa kuma zai tabbatar da cewa an cigaba da ciyar da ɗaliɓai don basu kwarin gwiwar koyo.
