Ɗan wasan ƙungiyar kwallon kafa ta PSG, kuma ɗan ƙasar Brazil Neymar,na fuskantar ƙalubale bayan da hukumar tattara harajin ƙasarsa ta Brazil ta kwace gine-ginensa da dama a ƙasar da wasu kadarori da ya mallaka, saboda samunsa da laifin shafe tsawon lokaci ba tare da ya biya harajin da ake binsa ba. Hukumar tattara harajin ta Brazil dai ta bayyana cewa adadin harajin da Neymar ya ƙi biya ya kai fam miliyan 14,dan hakane ta kwace gine-ginensa da sauran kadarorin sa da suka kai 36 har sai ya biya abinda ake binsa.
Sai dai kwace waɗannan kadarori ba wai yana nufin Neymar ba zai iya amfani da su bane, yana da damar yin hakan, amma matakin na nufin haramta mishi sayar da su ko kuma sanya su cikin wata huldar kasuwanci.
A cewar Jami’an tattara harajin Brazil, sun ce tarin harajin da ake bin Neymar na shekarar 2013 ne,lokacin da ɗan wasan ya sauya sheka daga kungiyar Santos ta kasar zuwa Barcelona dake kasar Sipaniya.
Kuma yanzu haka yana ƙungiyar kwallon kafa ta PSG dake ƙasar Faransa.