Wani mutum Mai suna Alh Idris ya fito da bindiga inda ya harbe wasu matasa mazauna unguwar Tudun maliki da suka shirya hawan doki wato kilisa.

Tun da fari dai Alh Idris sai da yayiwa matasan gargadi da kada su kuskura su biyo ta kofar gidansa a lokacin da suke yin kilisarsu.

Amma matasan basuji ba suka wuce ta kofar gidan ganin haka ne yasa Alh idris ya fito da bindiga ya dinga harbi a tsakanin mahaya dokunan.

Kakakin Rundunar yansandan jihar kano DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatarwa wakilin mujallar matashiya Ahmad Haysam faruwar lamarin, inda ya bayyana cewa a halin yanzu dai ya jikkata Akalla mutane 15 wanda suke asibiti a yanzu.
Shi kuma yan sanda sun nuna dabarun aiki sun kwace bindigar yanzu haka yana hannu ana bincikarsa daga bisani za’a gabatar dashi gaban kotu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: