Hukumar Hisbah ta jihar kano ta kai samame yankunan unguwa uku da rukunin unguwannin nassarawa.
Babban darakta a hukumar Mallam Abba Sufi shine ya bayyana hakan ga manema labarai yace sunyi nasarar kame mutane goma sha shida wadanda suka hadarda mata goma sha uku da maza uku.
Mallam Abba Sufi ya bayyana cewa hukumar zata tantance wadanda ta kamo domin daukan mataki na gaba.
Idan dai za a iya tunawa hukumar a dukkan samamen da tayi tanayin afuwa ga wadanda suke sabon Shiga a harkar ta yawace yawace.