Gwamnatin tarayya ta dakatar da shirinta na haramta Almajiranta a fadin kasa baki daya.

Mai magana da yawun shugaban kasa Malam Garba shehu ne ya bayyana hakan, inda yace gwamnatin kasar bazata aiwatar da matakin da tace zata dauka ba na haramta Almajiranci da barace barace.

Idan ba’a manta ba a baya bayannan akayi yunkurin hana almajiranta tun bayan da mai bawa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Manjo janar Babagana monguno mai ritaya, yace gwamnati na shirin haramta Almajiranci a Najeriya, don magance matsalar tsaro da kuma hana barace barace.

Sai dai kuma gwamnati ta bayyana cewa bazata aiwatar da matakin ba har sai ta kammala ganawa da dukkanin wadanda abin ya shafa da sauran masu ruwa da tsaki a harkar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: