Connect with us

Labaran jiha

Wata Sabuwa: Nasir Zango ya nemi ‘yansanda su kama mijin Hanan

Published

on

Wasika ga kwamishinan yansandan jihar Kano…

Bayan dubun gaisuwa da kyakyawan Fatan
alheri da addu’ar Allah yasa a gama lafiya nake
rubuta maka wannan budaddiyar wasika
domin ankarar dakai akan batun binciken matar nan da suka yi fada da mijin ta har fadan ya baci.
A gaskiya ana neman yin tuya amance da albasa, domin ni a fahimtata wannan al’amari fa rikici ne ya turnuke tsakanin miji da mata a cikin daki su kadai, har takai rikicin ya zama dauki ba dadi ta hanyar amfani da makami wajen kai hari da kare kai.
Daga maganganun su masu fadan na fahimci cewar an yi dambe a tsakani su, har takai an samu zubar da jini da kumburar mukamiki da kurjewar wasu sassa na jiki, rikici ne dai Wanda takai an sami casualties.
Har yanzu babu Wanda zai iya bayyana hakikanin abin da ya faru don hakan binciken ‘yansanda cikin tsanaki shine zai warware gaskiya a gane mahari da Wanda aka kaiwa hari, a fahimci Wanda aka kaiwa farmaki da kuma Wanda ya kare kansa, amma a yanzu a iya cewar magana ce ta kokawa a tsakanin mutum 2, Wanda bisa adalci su biyun ya kamata a kama a tuhume su da laifin tarzoma da tayar da husuma daga bisani a bambamce Wanda yafi laifi ko a sulhunta su a yafi juna ko kuma a kaisu kotu, To amma ya mai girma Kwamishina a yanzu naga ita matar kawai aka kama, domin shi mijin yana kwance a asibiti kuma naje banga ‘yansanda na gadinsa ba saboda kar ya arce, tunda a ka’ida ya kamata ace yana karkashin bincike akan tuhumar aikata laifi. Ya mai girma Kwamishina, kyale mijin tare da cigaba da tsare matar tamkar barin jaki ne ana barin taiki, ya kamata a dauki matakin da ya dace gudun kada mata suce kuna nuna musu wariya, ya mai girma Kwamishina, duk d
sanda mutane 2 suka yi fada ko wani ya kai kara duk biyun ake kamawa ace sun yi 2 fighting amma ga cikakken 2 fighting har an yi kare jini biri jini, amma yansanda sun kama sashe daya sun bar gudan, koda yake bansani ba ko nan gaba za a kamo daya barin. Babban abin da muke bukata shine adalci, a tsakanin kowa, amma yin haka zai kashe gwiwar mata suga kamar yansanda sun fi son kama mace idan tayi dauki ba dadi da namiji.
Allah ya bayyana gaskiya, Allah ya taimaki rundunar yansandan jihar Kano mai albarka.

Wasalam ka huta lafiya.

Nasiru Zango

1 Comment

1 Comment

  1. Hafsa

    June 25, 2019 at 3:10 pm

    Nagode maka Nasir zango. Wannan Shine batu na gaskiya.

Leave a Reply

Labaran jiha

Gwamnatin Jihar Yobe Za Ta Kwashe Mutanen Da Ambaliyar Ruwa Ta Shafa A Jihar

Published

on

Gwamnatin Yobe ta bayar da umarnin kwashe mutanen Usur da Gasma da ambaliyar ruwa ta yi wa barazana a kananan hukumomin Bade da Karasuwa.

Mataimakin gwamnan jihar, Alhaji Idi Gubana ne ya bayar da wannan umarni a jiya Lahadi a Gashua lokacin da ya ziyarci yankunan da ambaliyar ruwa ta shafa.

Ya umurci Hukumar bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar (SEMA) da ta kwashe mazauna Usur da Gasma zuwa sabon rukunin gidaje da aka gina a Jaji Maji.

Mataimakin gwamnan ya ce sun kai ziyarar ne domin jajantawa wadanda ibtila’in ya rutsa da su da kuma tantance irin ɓarnar da aka yi domin samun tallafin da ya dace.

Gubana ya kuma umurci hukumar da ta samar da kayan agaji ga wadanda abin ya shafa domin rage musu raɗaɗi.

A nasa jawabin, Sarkin Bade, Alhaji Abubakar Suleiman, ya gode wa mataimakin gwamnan bisa ziyarar jaje da ya kai musu.

Ya kuma bukaci al’ummar garuruwan da su yi addu’ar Allah ya dawo da zaman lafiya a yankunan da lamarin ya shafa.

Mataimakin gwamnan ya samu rakiyar kakakin majalisar dokokin jihar Yobe, Alhaji Ahmad Mirwa da sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Baba Wali da dai sauransu.

Continue Reading

Labaran jiha

Gwamnatin Jihar Kaduna Za Ta Hukunta Wadanda Su Ka Kashe Fulani Biyu

Published

on

Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El’Rufa i ya yi Allah wadai da hallaka wasu fulani Makiyaya biyu tare da kone su a cikin karamar hukumar Birnin Gwari ta Jihar a ranar Lahadi.

Kwamishinan Tsaro da harkokin cikin gida Samuel Aruwan shi ne ya tabbatar da faruwar lamarin.

Sanuel Aruwan ya ce bayan faruwar lamarin an aike da jami’an tsaro domin kamo wadanda su ka yi aika-aikar.

Batagarin sun hallaka fulanin ne sakamakon zarginsu da su ke na yi na yin garkuwa da mutane.

Aruwan ya ce gwamnatin Jihar za ta yi wata ganawa da iyalan wadanda aka hallaka domin yi musu ta’aziyya.

Sannan ya kara da cewa an hallaka Makiyayan ne a lokacin da su ka shiga cikin karamar hukumar Birnin Gwari domin yin siyayyar kayayyaki.

Ya ce zuwan su ke da wuya su ka farwa Fulanin tare da kiran jami’an tsaro.

Aruwan ya ce bayan jami’an tsaron sun isa gurin matasan yankin su ka kwace mutanen su ka kashe su tare da kone su.

Continue Reading

Labaran jiha

Wata Kotu Ta Daure Wani Mutum Kan Yunkurin Sayar Da ‘Yarsa A Jihar Legas

Published

on

Wata babbar kotu da ke Jihar Benue ta bayar da izinin garkame wani mutum wanda yayi kokarin sayar da ‘yarsa akan kudi Naira Miliyan 20.

Jami’an rundunar ‘yan sandan Jihar su ne wadanda su ka gurfanar da wanda ake zargin shi da abokinsa a gaban kotun.

Jami’an sun ce abokin nasa shine wanda ya taimaka masa wajen hadin baki domin a siyar da yarinyar da kuma safarar mutane.

Jami’ar ‘yar sanda mai gabatar da kara ta bayyana cewa an kama mutanen ne a lokacin da su ke kokarin sayar da yariyar mai shekara hudu.

Ta ce ana tsaka da cinikin yarinyar su ka kama mutanen yayin da mutumin da za su sayarwa da yariyar ya tsere.

Jami’ar ta kuma bukaci kotun da ta yanke musu hukuncin sakamakon karya wasu dokokin da su ka saba dokar Jihar.

Bayan gabatar da karar Alkaliyar kotun ta aike da su gidan yari zuwa ranar daya ga watan Disamba domin ci gaba da da shari’ar.

Continue Reading

Talla

Trending

%d bloggers like this: