Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo yayi kira ga yan Najeriya dake zaune a kasashen waje da suyi watsi da yawa-yawan labaran da ake cewa wai garkuwa da mutane ya addabi mutanen Najeriya.
Osinbajo ya bayyana hakan ne a lokacin da yake tattaunawa da yan Najeriya a birnin New York ta kasar Amurka,
Inda ya kara da cewa babu gaskiya a mafi yawan maganganun da ake yi, ”
Sai dai ya danganta lamarin da siyasa ce kawai ba kamar yadda kuke ji a kafafen yada labarai ba”.
Osinbajo yace ” Eh tabbas ana samun garkuwa da mutane jifa-jifa amma ba wannan ne farau ba.
A cewar sa yace Bari ma kuji duk rahotanni da labaran da kuke ji a kafafen yada labarai wai an sace wancan, anyi garkuwa da wancan duk ba gaskiya bane, siyasa ce kawai kuji in gaya muku.
” Akwai wanda za ka ji wai anyi garkuwa da su, amma dai wasu labaran da zaka ji, kai ma kasan zuki ta malle ne, ba haka bane. Sannan a duk lokacin da aka kawo labarin wai an yi garkuwa da wani sai munyi bincike sosai, amma daga karshe sai mugano ashe hira ce ta mutane ba gaskiya bane.
Sai dai mataimakin shugaban kasar Ya ce gwamnati na iya kokarinta wajen ganin an shawo kan matsalar tare da kawo karshen matsalolin tsaro a fadin Najeriya.

Madogara -muryar yanci/NAN

Leave a Reply

%d bloggers like this: