Dambarwar siyasar Kano wadda ‘yan magana ke cewa sai ‘yan Kano na cigaba da daukar sabon salo a lokacin da Gwamna Ganduje ke cigaba da jan ragamar mulkinsa a karo na biyu, inda tsagin jam’iyyar adawa ta PDP da dan takararta Abba Kabir Yusuf ke kalubalantar zaben gwamnan karo na biyu a gaban kotu.

General Idris Bello Dambazau mai ritaya daya ne daga cikin manyan jiga-jigai a tafiyar Kwankwasiyya a baya, biyo bayan juyin juya halin zaben shekarar nan da muke ciki da ta maida su General Dambazau din zuwa gidan siyasar Gandujiyya da ludayinta ke kan dawo.
General Dambazau ya wallafa wata magana a shafinsa na Facebook a daren yau bayan ya saka wani hotonsa a kishingide, kamar yadda kuke gani a hoton dake kasa, inda yake nuna cewa duk wanda ya kalleshi ya san fa hakika yafi tsohon gwamnan Kano jagoran darikar Kwankwasiyya Engr. Dr. Rabi’u Musa Kwankwaso koshin lafiya.


Mutane da dama ne dai suka bibiyi wannan batu na dambazau suka kuma yi tsokaci akai, shin ko yaya kuke kallon wannan batu?