Kwamandan hukumar dake yaki dasha da fataucin miyagun kwayoyi ne Reshen jihar kano Dakta Ibrahim Abdul ya bayyana cewa gwamnatin jihar kano karkashin gwamnan kano Abdullahi Umar Ganduje, da sarkin kano Muhammad sunusi ll suna ba wa hukumar gudunmawa ta musamman don magance matsalar shaye shaye a jihar kano.

Wannan ne yasa gwamnan sai da ya turo wayanda ake son nadawa a matsayin kwamishinoni dun bincikarsu ko suna ta’ammali da kwayoyi.
Ibrahim Abdul ya kara da cewa a baya ma sarkin kano ya sa an binciki hakimansa wanda duk aka samu yana ta’ammali da kwayoyi aka sauke su.

An samu cigaba sosai wajen magance matsalar shaye shaye a jihar kano a cewar kwamandan kasancewa a baya ana kama kayan maye Ton ton ne sai gashi a halin yanzu kilogram ake kamawa.

Wannan yasa a baya kano itace ta daya a jihohin Najeriya da suka fi ta’ammali da kwayoyi amma yanzu Lagos ne sai Jihar Oyo na biyu kano ce a matsayin na 3 wanda a baya itace ta daya, wanann ba karamin nasara bane, kuma bazamu yi kasa a gwiwa ba zamu cigaba da kokari wajen dakile wannan matsala a jihar kano,a cewar Dakta Ibrahim Abdul.
Duk wannan bayanai yana kunshe ne duk a kokarin hukumar na bayyana irin matakin da shaye shaye ke ciki a jihar kano a dai dai lokacin da ake gudanar da bikin ranar Shaye shaye ta duniya.
Majalisar dinkin duniya ce ta ware duk Ranar 26 na watan yuni a matsayin ranar bikin yaki da shaye shaye, a jawabin nasa da ya gudanar a safiyar yau a gidan Radiyon freedom kano, Dr Ibrahim ya ce taken bikin bana shine YIWA LAFIYA ADALCI TARE DON CETO RAYUWA.
Za’a cigaba da wayar da kai tare da kira kan illar shaye shaye a dakin taro na Murtala Muhammad Labrare.