Shugaban kasar Venizuela Nicolas Maduro yayi barazanar saka kafar wando daya da yan hamayyar kasar muddin suka cigaba da barazanar kifar da gwamnatinsa.

Maduro ya bayyana hakan ne ta cikin bayanin da yayi wa Al’ummar kasar ta kafafen yada labarai, inda yace babu shakka zai samar da wani yanayi na juyin juya hali a kasar muddin yan hamayya suka cigaba da matsa masa lamba.

Tun da farko kakakin Nicolas Maduro yayi ikirarin cewa tsoffin jami’an yan sandan kasar da sojojin kasar suna shirin tada Bom a fadar gwamnatin kasar, tare da kwace babbar birnin kasar (Caracas) da kuma wawure kudaden bankin babbar kasar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: