Mujallar Matashiya

Mai Tsage Gaskiya Komai Ɗacinta

Talla

Siyasa

Zan siyar da kadarorina don biyawa matasan jihar Kano kuɗin Makaranta – Kwankwaso

Tsohon Sanata Rabi u Musa kwankwaso ya bayyana takaicinsa matuƙa na ganin koma baya da jihar Kano ta samu musamman a fannin Ilimi.

Kwankwaso ya bayyana cewa duk da ba su da gwamnati szai yi wani yunƙuri na siyar da kadarorinsa baki ɗaya don biyawa matasa kuɗaɗen makaranta.

Cikin wata hira da ya yi da manema Labarai kwankwaso ya nuna damuwarsa matuƙa na yadda aka rufe wasu makarantu a jihar Kano kamar yadda ya bayyana hakan a matsayin rashin kishin jihar.

Kwankwaso ya ce ya siyar da wani filinsa da aka bashi a Sokoto kuma yana da wasu a kaduna Da sauran jihohi kuma duk ya sakasu a kasuwa don karɓar kuɗin tare da biyawa mutane kuɗin makaranta.

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *

%d bloggers like this: