sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha ya bayyana cewa shugaban kasa muhammad Buhari na shirye shryen sanar da sunayen sabbin ministocinsa.

Boss ya bayyana cewa Shugaban kasa Muhammadu Buari zai sanar da ministocinsa a watan Yuli, yace hakan zai zo ne bayan yan majalisu sun dawo daga hutun da suke a yanzu.
Sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha a ranar Alhamis, 27 ga watan Yulin 2019, Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai sanar da sunayen ministocin fadarsa Aso Rock dake Abuja.
A cewar jaridar The Guardian, Mustapha ya bayyana cewa za a kaddamar da sabon majalisar Buhari da zaran yan majalisu sun dawo daga hutu.
Ya kara da cewa shugaba Buhari zai gabatar da lamarin gaban majalisar dokokin tarayya ba tare da bata lokaci ba.
Sabanin hasashen da ke yawo a tsakanin ‘yan Najeriya, ba lallai ne a kafa majalisar Shugaban kasa Muhammadu Buhari ba kan watan Oktoba, musamman duba ga barazanar da ‘yan majalisar tarayya suke yi na kaurace ma majalisar dokokin har sai an biya su alawus dinsu.
Jaridar Guardian ta ruwaito cewa makonni biyu bayan rantsar da yan majalisun dattawa da majalisar wakilai, majalisar dokokin tarayya ba’a biya su alawus da hakokin su ba, wanda doka ta tanadar a basu. Ana ganin wannan ka iya kawo nakasu a aikin majalisun biyu.

