Connect with us

Labarai

Shekaru 23 da kafuwar Ganduje Foundation, Gwamna Ganduje ya yi kira ga shugabanni su yi koyi da wannan cibiya

Published

on

 

Daga Abba Anwar

Yau shekaru ashirin da uku (23) kenan da kafa Gidauniyar Ganduje, wato Ganduje Foundation. A shekarar 1996 ne Dr Abdullahi Umar Ganduje ya yi tunanin samar da wata mikakkiyar hanya da zai kara inganta harkokinsa na tallafawa al’umma ta bagarori da daman gaske.

Ta fuskar ilimi ne, musamman ilimin Addinin Musulunchi, da kuma bangaren tallafawa harkokin lafiya da tsafar muhalli. Sai kuma uwa uba, harkar tallafawa Addinin Allah, Musulunci, ta hanyar shigo da maguzawa cikin da’irar Musulunchi.

Ya yi wannan kyakkyawan tunani ne tun ma kafin ya zama Mataimakin Gwamna ko ma Gwamna. Wanda hakan ya ke nuni da korewar wani sofane na siyasa a cikin al’amarin gaba daya. Saboda Allah a ka yi nufi da wannan kyakkyawan aiki, kullum sai kara samun tagomashi ayyukan wannan Gidauniya suke yi.

Hakan shine yake nuni da cewa, tun tale-tale dama akwai wannan kishi na al’ummarsa a cikin zuciyarsa. Daga cikin abubuwan da su ka ba shi sha’awa game da wannan kyawawan ayyukan Gidauniyar ta sa, sun hadar da yadda wasu hamshakan mutane a ciki da wajen kasar nan ke aiwatar da ayyukan alheri ta irin wadannan hanyoyi.

Kamar a wata hira ta musamman da wasu ‘yan jarida na kasashen duniya su ka niko gari daga kasashe daban daban su ka zo, don ganawa da shi game da harkokin wannna Gidauniya ta sa, ya ce “Abin ya na ba ni sha’awa matuka da gaske idan na ga mutane masu kishin al’ummarsu su na da ire-iren wadannan Foundations din don tallafawa jama’arsu.”

Su wadancan ‘yan jarida da su ka zo, sun ce sun yi bincike ne mai tsananin gaske wajen zakulo ayyukan wannan Gidauniya ta Ganduje. Kuma abinda ya kara ba su sha’awa shine, shigar Ganduje cikin harkokin mulki, bai hana shi gudanar da ayyukan wannan Gidaumiyar ta sa ba.

Saboda bayar da muhimmanci ga harkar ilimin Addinin Musulunci hakan ya sa wannan Gidauniya ta yi uwa ta yi makarbiya wajen giggina makarantun Islamiyoyi da kuma gyara ajujuwan wasu gami da tallafawa harkar lafiyar dalibai masu karatu a wadannan makarantun.

Tushen farko na ilimi a Musulunchi shine Masallachi. Saboda fahimtar hakan ta sa Ganduje ya gina Masallatai sama da guda 20 daga lokacin kafa wannan Gidauniya kawo yanzu.

Daga baya bayan nan akwai Masallatai da ya yi a cikin jami’o’in Bayero dake Kano da kuma ta Kimiyya da Fasaha ta Wudil. Sannan ga wani katafaren Mallachin Juma’ din dai a cikin kasuwar Kwari a birnin Kano.

Masallatan da wannan Gidauniya ta gina sun fantsama a bangarorin jihar da yawan gaske. Wannan shi ya ke nuni da cewar Baba Ganduje ya damu matuka da ainihin tushen mafificin ilimi na addinin Musulunchi, wato Masallachi.

Saboda kuma ya kara assasa karantarwar Littafin Allah Mai Tsarki, wato Al’Qur’ani, tsakanin yaranmu, sai da wannan Gidauniya ta Ganduje ta sa tsarin wata Musabaqa, wato gasar karatun Littafi Mai Tsarki, wanda a na yi tun daga matakin kananan hukumomi zuwa shiyya shiyya har zuwa kuma matakin jiha.

A dalilin wannan gasa ne da kuma kara tallafawa makarantun Islamiyya, a halin yanzu yara daruruwa sun kwarance matuka wajen iya karanta Al’Qur’ani da Tajwidi tare da kuma sanin ma’anonin abubuwan da suke karantawa.

Gidauniyar Ganduje ba wai a cikin jihar Kano kawai ta tsaya ba wajen tallafawa Masallatai da makarantun Addini, abin har ya kai ga wasu jihohin da kuma cikin kasar Nijar ma, makwabciyarmu. Daga cikin abubuwan da su ka kara jan hanakalin wadancan ‘yan jaridu na kasashen waje da su ka zo don tattaunawa ta musamman da Dr Ganduje kenan.

Ba kuma kawai kara kyautata yanayin makarantunmu na Islamiyoyi ba kawai, ita wannan Gidauniya ta na kan kara alkinta hanyoyin zamanantar da yanayin koyo da koyarwa na wadannan makarantu.

Ganduje ya ce, “Babban abinda muke son cimma shine, kara tabbatar da wanzuwar ayyukan wannan Gidauniyar. Saboda abin alheri irin wannan da a ka fara bai kamata a bar shi ya kwaranye ba saboda tsawon lokaci.”

Game da Musuluntar da Maguzawa kuma, wannan Gidauniya ta Musuluntar da su sama da Dubu Ashirin (20,000). Wanda wannan ba karamar nasara ba ce a cikin wannan Addini namu na Musulunchi.

“Dukkan wadanda Allah Ya sa mu ka musuluntar, mu da hotunansu, da wuraren da suke zaune da sunayensu na da da kuma sababbin sunayensu bayan sun karbi Kalma. Alhamdulillah da Allah Ya sa ta hayarmu ne za su karbi Kalmar Shahada,” in ji Ganduje.

Wajen taimakon masu lalurar ido kuma wannan Gidauniya ta tallafawa masu wannan lalura sama da su Dubu Ashirin (20,000). Wadanda a ka taimakawa wajen maganta lalurorinsu na ido sun fito ne daga bangarori daban daban na wannan jiha. Wadansu an yi musu aiki, wasu kuma an ba su magana. Wasu kuma an yi musu gilasan ido.

A waccan tattaunawa Ganduje ya ce “Alhamdulillah daga cikin irin mutanen da a ka yi wa aikin ido akwai wani bawan Allah wanda ya kai kimanin shekaru 30 ba ya gani, amma cikin taimakon Allah yanzu Allah Ya ba mu damar taimakonsa ya samu idanunsa tangaran.”

Ba wai kuma lalurar idanu kawai wannan Gidauniyar ta ke taimakon jama’a da shi ba. Akwai wani tsarin taimakawa marasa lafiya kala-kala da wannan Gidauniya ta ke fita daga lokaci zuwa lokaci ta na duba wadansu nau’in cututtuka na al’umma saboda taimaka musu.

Abinda kuma ya shafi harkar marayu da gidajen yara, wannan Gidauniya ta na kai abinci a kai a kai irin wadannan gidajen. Wannan kuma bai rasa nasaba da yadda Dr Ganduje ya yi karatun addini har ya fahimci muhimmancin tallafawa marayu da kuma irin gwaggwaban ladan da ke tattare da hakan.

Babban fatan Khadimul Islam, Dr Abdullahi Umar Ganduje shine, shugabanni su dinga koyi da wadannan ayyuka na alheri. Ya ce “Babban fatanmu shine, a samu wani gungu na shugabannin al’umma da su yi koyi da irin wadannan ayyukan alheri. Ko ma saboda yadda wannan addini namu mai albarka ya yi horo da taimakon al’umma.”

Anwar shine Babban Sakataren Yada Labarai na Gwamnan Jihar Kano
Lahadi 30 ga Watan Yuni, 2019

Click to comment

Leave a Reply

Labarai

An Kone Ofishin Yan Sanda A Anambra

Published

on

Wasu ƴan daga sun kai hari tare da ƙone ofishin ƴan sanda a jihar Anambra.

 

An kai harin ne ofishin ƴan sanda na Neni da ke ƙaramar hukumar Anaocha a jihar da misalin ƙarfe 02:00am na dare wayewar yau Alhamis.

 

Mai magana da yawun ƴan sanda a jihar Tochukwu Ikenga ya ce mutanen sun kai harin ne da abin fashewa da ake zargi bam ne.

 

Sannan ya ce maharan ba su ɗauki makaman jami’an ko yin garkuwa da jami’an su ba.

 

Ya ƙara da cewa, maharan sun gudu bayan da ƴan sanda su ka ci ƙarfinsu.

 

Zuwa yanzu ana ci gaba da hibiya don gano su waye su ka kai harin tare da kamasu.

 

Sai dai bai bayyana asarar da aka yi ba a sakamakon harin da aka kai.

 

 

Continue Reading

Labarai

An Kama Ƴan Fashin Da Su Ka Yi Wa Matar Aure Fyaɗe A Jigawa

Published

on

Rundunar ƴan sanda a jihar Jigawa sun kama wasu mutane uku da ake zargi da aikata fashi da makami haɗi da fyaɗe ga matar aure a jihar.

 

Kwamishinan ƴan sandan jihar AT Abdullahi ne ya bayyana haka yau Alhamis.

 

Ya ce an kama mutane uku bayan da su ka shiga gidan wani Mudan Ibrahim mazaunin ƙauyen Chori a ƙaramar hukumar Ringim tare da yi masa fashi daga bisani su ka yi wa matarsa fyaɗe.

 

Ƴan sandan sun samu labarin ne a ranar 17/03/2024.

 

Bayan zurfafa bincike, jami’an sun kama wani Umar Ibrahim, Umar Nasara, da wani Abubakar Isah dukkaninsu mazauna ƙauyen Chori a jihar.

 

Tuni aka ci gaba da zurfafa bincike a kai, kuma da zarar an kammala za su gurfanar da su a gaban kotu kamar yadda kwamishinan ya shaida.

 

A wani labarin kuma kwamishinan ya bayyana nasarar kama wasu ƴan fashi da makami, da kuma wasu da ake zargi da aikata sata a jihar.

 

 

Continue Reading

Labarai

Malamin Makaramtar Firamare Na Kuriga Ya Mutu A Hannun Ƴan Bindiga Kafin Kuɓutar Da Dalibai

Published

on

Gwamnan jihar Kaduna Malam Uba Sani ya sha alwashin ɗaukar nauyin karatun ɗalibai 137 da aka kuɓutar daga hannun ƴan bindiga.

 

Ɗaliban su ne waɗanda aka yi garkuwa da ssu daga makarantar firamare ta Kuriga a jihar.

 

Gwamnan ya ce zai ɗauki nauyin karatun nasu ne daga matakin Firamare zuwa sakandire ƙarƙashin cibiyar Uba Sani Foundation.

 

Gwamnan ya bayyana haka yau Alhamis kafin mayar da ɗaliban zuwa Kuriga.

 

Ya ce bayan kuɓutar da su, an ɗauki lokaci domin duba lafiyarsu kafin miƙasu ga iyayensu.

 

Ya ce guda cikin malaman da aka yi garkuwa da su mai suna Malam Abubakar, ya rasa ransa a hannun ƴan bindigan.

 

A sakamakin haka, gwamnan ya ce zai ɗauki nauyin karatun ƴaƴan malamin, tare da bai wa iyalansa naira miliyan goma.

 

Akwai waɗanda su ka samu larurar kwakwalwa daga cikin ɗaliban da aka kuɓutar, a don haka su ka miƙasu ga kwararrun likitoci domin duba lafiyarsu.

 

Sannan gwamnatin ta bayar da umarnin yin wasu ayyuka a Kuriga, wamda gwamnan ya ce garin na daga cikin garuruwan da su ka fi zaman lafiya a jihar.

 

 

 

 

Continue Reading

Talla

Trending

%d bloggers like this: