Shugaban kasa muhammad Buhari, ya kadu matuka da jin mutuwar Mataimakin shugaban Editocin Najeriya Mal Umar Sa’id T/wada.

A cikin wata sanarwa da kakakin gwamnatin Mal ,Garba shehu ya fitar Abuja, inda ya bayyana Umar T/wada a matsayin jajirtaccen, dan jarida da yake aiki kan ka’idoji tare da bin dokokin aikin jarida.
Inda kuma shugaba buhari ya mika ta’aziyarsa ga iyalansa da yan uwa kan Allah ya jikansa da Rahama.

Sannan kuma ya bayyana cewa mutuwar ba iyalansa kawai ya shafa ba, harda Alummar Najeriya baki daya kasancewar sa abin koyi kan kyawawan halayensa, da kuma jajircewa akan aikinsa.
