Shugaban ƙasar Amurka Donald J Thrump ya gargaɗi ƙasar Iran kan gwajin makamin ƙare dangi da za ta yi.

Ƙasar Iran na shirin gwada makamin ne saɓanin yarjejeniyar da suka cimma matsaya da ƙasar Amurka a shekarar 2015.
Shugaban ƙasar Iran Hassan Rauhani ya ce za su ƙara nisan zangon makamin kamar yadda ;suke buƙata.

Sai dai shugaba Donald Trump ya gargaɗesu da cewar muddin suka sauka daga matsayar da suka yi a baya za su dɗauki mummunan mataki a kansu.
