Abin nufi shi ne daga lokacin da aka sanar da dokar idan aka kama mutum yana haya da adaidaita sahu za a hukuntashi.

Gwamnatin jihar Anambra ta dakatar da hayar adaidaita sahu a faɗin jihar.

Kwamiahinan sufuri a jihar Mr Uchenna Okafor ne ya bayyana hakan ga manema labarai yana mai cewa, daga lokacin da aka sanar da dokar muddin aka samu mutum yana hayar adaidaita sahu wato babur mai ƙafa uku za a hukunta shi.

Kwamishinan ya umarci jami an tsaro da su fatattaki masu baburan don barin jihar bisa matsaloli da ya ce suna haddasawa a jihar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: