Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya jaddada yunƙurinsa ganin an inganta harkar lafiya a faɗin jihar baki ɗaya.

Gwamnan ya ce zangon mulkinsa na biyu harkar lafiya na sahun gaba gaba don ganin an maganace rashin wadatar asibitoci a faɗin jihar.

Cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran gwamna Kano Abba Anwar ya fitar,  gwamnatin ta shirya samar da asibitocin kwanciya mai ɗauke da gadaje 400 a dukkanin masarautun Kano.

Cikin jawabinsa Gwamna Abdullahi Ganduje ya jaddada aniyarsa na samar da ilimi kyauta a jihar tare da kammala ayyukan titin wanda ta gada daga gwamnatin da suka shuɗe.

Sannan ya nemi goyon bayan al umma da su kasance masu taimakawa gwamnatin ta kowacce hanya ta yadda za a tabbatar da cigaba mai ɗorewa a faɗin jihar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: