Ƙungiyar mata  ta ƙasa ta kai ƙarar  ɗan majalisar nan  Elisha Agbo zuwa majalisar  ɗinkin duniya , bisa zargin sa marin wata mace mai shayarwa a wani shago  dake birnin Abuja a lokacin da yaje siyayya.

Rahotanni dai sun tabbatar da cewa cacar  baki ne ya kaure a tsakanin Matar mai shayarwa da ɗan majalisar Dattawan Elisha daga bisani zafin zuciya ya debe shi inda ya mare ta a fuska.

Ƙungiyar matan shiyyar Abuja ta buƙaci majalisar dinkin duniya da sauran ƙungiyoyi n kare hakkin bil Adama na majalisar da su shiga maganar zargin cin zarafin matar auren da ɗan majalisar dattijai daga jihar Adamawa yayi mata a wani shago.

A ranar juma’ar  da ta gabata ne rundunar  yan sanda shiyyar birnin tarayya Abuja ta bada belin dan majalisar bayan an tsare shi tsawon sao’I 24 ana tuhumarsa.

Anata ɓangaren shugaban kula da kare hakkin mata dake Abuja Hadiza Umar ta bayyana cewwa har yanzu basu karɓi afuwar da ɗan majalisar ya nema a gurinsu ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: