Ƙungiyar matan shugabannin Afrika dake halartar taron ƙasashen nahiyar Afrika (AU) a jamhuriyar Nijer sun buƙaci a tsaurara haraji kan abubuwan dake haddasa cutar kansa musamman Taba sigari da kuma Barasa.

Uwar gidan shugaban ƙasar Burkina Faso SIKA KABORI, wacce itace ta wakili takwarorinta na sauran kasashen Afrika wajen bayyana wannan buƙata a taron dake gudana a ƙasar Nijer.
A cewarta Binciken masana yace aƙalla mutane miliyan tara ne ke mutuwa a duk shekara sakamakon kamuwa da cutar kansa, kuma kashi 70 cikin 100 daga cikinsu sun fito ne daga kasashe suke masu fama da talauci.

Matan shuwagabannin Afrika sun koka matuƙa kan yadda Taba sigari da barasa ke da matuƙar sauƙi a nahiyar Afrika, saɓanin yadda abin yake a nahiyar turai, don haka suka ɓukaci a tsaurara matakai ta hanyar ƙara haraji akan Taba sigari da kuma barasa domin suyi wahalar sa mu a wurin masu amfani dasu.
