Ƙasar masar ta tabbatar da sallamar mai horar da ƴan ƙungiyar kwallon kafa ta kasar biyo bayan rashin nasara da ƙasar tayi a hannun ƙungiyar kwallon kafa ta Afrika ta kudu da ci daya mai ban haushi.

Ƙasar masar itace mai karɓar baƙoncin gasar kwallon kafa ta nahiyar Afrika dake gudana a halin yanzu, sai dai Tuni ƙasar Afrika T Kudu ta fitar da masar din daga gasar a zagaye na biyu.
Magoya bayan ƙasar masar dai sun nuna bacin ransu kan rashin nasara da sukayi a gasar kasancewar sune masu masaukin baƙi.

Sai dai sun nuna goyon bayan su ɗari bisa ɗari ga ƙungiyar kwallon kafa ta Najeriya wacce a halin yanzu ta tsallaka zuwa mataki na kusa da kusa dana ƙarshe wato( quarter final) tun bayan da ta lallasa ƙasar Kamaru da ci 3-2.
