Ƴan bindiga a jihar zamfara sun saki wasu Karin mutane goma sha ɗaya da suka yi garkuwa da su a wani  mataki na fara cimma yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin ƴan bindigar da bangaren gwamnatin jihar har ma rundunar  ƴansanda jihar.

A baya bayan nan dai gwamnan jihar zamfara Mohammad Bello Matawalle ya bayyana shirinsa na yiwa ƴan bindiga Afuwa  amma sai sun yarda sun ajiyye makamansu.

Mutanen da aka saki sun shafe watanni biyu a hannun ƴan bindigar tun da akayi garkuwa dasu, tuni kwamishinan yan sandan jihar Zamfara Usman Nagogo  ya karɓi  mutanen a dajin gidan dawa dake kusa da ƙaramar hukumar ƙaura Namoda  a jihar zamfara.

A watan Afrilun da ya gabata jami’an tsaron sa kai wato Vigilante a jihar zamfara ta sako wasu fulanin 25 da suke tsare da su daga bisani ƴan bindigar suma suka saki mutum 15 wanda sukayi garkuwa dasu a wani matakin kawo ƙarshen  matsalar tsaro a fadin jihar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: