Sabon shugaban kamfanin man fetur na Ƙasa Mele Kyari ya bayyanawa shugaban majalisar dattawa Ahmed Lawan cewa sauƙin man fetur ne ya sa ake shigo da kaya sake babu ƙaidi cikin ƙasar.

Yayin wata ziyara da ya kaiwa shugaban a ofishinsa da ke majalisar ya bayyana cewar ƙasar Najeriya ita ce ƙasa mafi siyar da man fetur a rahusa idan aka yi la akari da sauran ƙasashen Africa.

Ya ce abu ne mai matuƙar wahala a cigaba da siyar da man futur ɗin a farashin 145 na kowacce lita.

Leave a Reply

%d bloggers like this: