Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa INEC ta fara shirin tsara zaɓen 2023 mai zuwa.

shugaban hukumar na ƙasa faefesa Mahmood Yakubu ne ya shelanta hakan yayin taron masu ruwa da tsaki da ya gudana a Ikeja jihar Legas.

Ya ce hukumar ta fara shirin tsara zaɓn 2023 tare da duba kura kuren da aka samu na 2019 don gyarawa.

Sun gudanar da makamancin wannan taron a Abuja inda aka zauna da masu ruwa da tsaki na hukumar zaɓe, ƴan jarida jami an tsaro da wasu daga cikin yan jam iyyu.

Taron ya samu halartar kwamishinonin zaɓe na jihohin Najeriya da sakatarorin hukumar kamar yadda kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya rawaito.

Leave a Reply

%d bloggers like this: