Kamfanin mai a Najeriya NNPC ya musanta labarin da ke nuni da ƙara farashin litar mai a Najeriya.

Cikin wata sanarwa da suka aike ga yan Jarida, kamfanin ya ce shugaban kamfanin ya gana da shugaban majalisa amma ba su tattauna kan batun ƙara kuɗin ba.
Haka kuma sun buƙaci a yi watsi da waccen magana wadda suka ce ba su san tushenta ba.

