Shugaban mujallar Matashiya Abubakar Murtala Ibrahim ya bayyana cewa Ƴaƴan marasa tarbiyya ne ke hallaka mazajensu

Batun da ke yawo a yanzu bai wuce yadda mata ke yunƙurin hallaka mazajensu ba wasu ma su hallakasu gaba ɗaya.

Babu shakka ko tantama babu mace mai tarbiyya tare da sani Allah da bin umarninsa da za ta taɓa kawo tunanin yadda za ta hallaka mijinta ko nakastashi.
Mafi yawan abubuwan da ake tunani suna kai mace ga irin hakan bai wuce matun kishiya ko auren dole ba, idan muka duba a baya ko ita kanta macen da ke ƙoƙarin hakan mata nawa babanta yake da su? Da yawan auren da ake yi da wani ma bai san matarba za a ɗaura masa kuma ko yaji ba lallai ka taɓa ji ta yi ba, ba ina nufin auren dole na da kyau ba sai dai irin tarbiyya da biyayyar da ake yi kuma har a yanzu ana samun haka.
Idan ka ɗauki macen da zata nakasta maƙarfafar mijinta tabbas za ta iya kasheshi ko ma na ce ta kasheshi a tsaye kuma duk mutumin da zai yi hakan babu alamar imani a zuciyarsa.
Allah ya kan jarrabi mutum amma a lokuta da dama Allah na taimakon mutum ne bisa niyyar da ke zuciyarsa.
Allah ne ya ce a yi aure, kuma batun ƙara aure mafi yawa daga cikin maza na ƙarawa ne saboda rashin jin ɗdaɗin zama da uwargidansu, da za ki masa biyayyar da za ki mallakeshi ko sha awar wata bazai yi ba balle ya ce zai ƙara aure saboda maza na buƙatar nutsuwa a koda yaushe.
Idan ka ɗauki gidan da babu tarbiyya a nan ne za ka ga yarinya taga yadda babarta ke shaƙe babanta a kan kuɗin cefane ko kuma ƙin bin umarninsa.
A ƴan kwanakinnan mazaje da yawa sun kwanta dama a kan haƙƙin da Allah ya basu, ga abu nai ciwon gaske ka auri mace ka ganta na bibiyar maza a waje, ka ƙaddara a kanka cewa kana da budurwa ka je zance kaga wani ya zo ya kakeji a ranka, to baka fa aureta ba ma kenan ina ga ta zama malakinka ka ganta tana tarayya da wasu mazan.
Akwai buƙatar mazaje a kula sosai don samo irin macen da za ka aura.
Shi kuwa mutum mara tarbiyya idan ya yi ɗanyen aiki komawa ake zuwa ga kundin da ya halatta aure a masa hukunci dai dai da abinda ya aikata idan ta kashe a kaaheta haka Allah ya ce idan kuwa aka barta za ta gurɓata ƙasa ta jawo mafsifu kala kala a doron ƙasa, malamai ne auka faɗa.
Idan ta lahantashi a lahantata ko kuma ɗaukar hukuncin dai dai da abinda ta aikata.
Allah ya saka tausayin mata a zuciyar maza amma hakan ba yana nufin su aikata duk abinda suke so a kyalesu ba, maza ke fita yaƙi saboda raunin mace amma ta samu damar kashe maza don bata san tsadar jininsu ba.
Allah ya kiyayemu ya shiryemu bisa kura kuren da mukai.
Abubakar Murtala Ibrahim
10 11 1440
13 7 2019

Leave a Reply

%d bloggers like this: