Ƙungiyar na shirin ɗaukan matakin ne muddin gwamnati ta cigaba da ƙin biyan sabon tsarin albashin mafi karanci dubu talatin ga ma’aikatan ƙasar nan.

Sabon shugaban ƙungiyar  kwadagon ta kasa TUC  Kadiri  olalayi shine ya tabbatar da hakan, inda ya bayyana cewa ƙungiyar tana shirye shiryen matakin da zata ɗauka anan gaba.

A baya dai kwamitin dake sasanta tsakanin gwamnati da ƙungiyar ta kwadago taki amincewa da buƙatar da gwamnatin tarayya  ta bayar  cewa zata ba ta akalla kaso 9 cikin dari  na albashin dake aiki a mataki na 7 zuwa mataki na 14 sai kuma   kaso 5  dake aiki a mataki na 5 zuwa mataki na 17.

Leave a Reply

%d bloggers like this: