Gwamnan jihar kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya sake nanata ƙudurin gwamanatinsa  na kawar  da barace barace da gararambar almajirai akan titian jihar.

Ganduje ya bayyana hakan ne A lokacin da yake karɓar baƙoncin shugaban  masu rinjaye  a majalisar tarayya  kuma ɗan majalisa mai wakiltar Doguwa da Tudunwada Alhassan Ado Doguwa a fadar gwamantin  kano.

Gwamnan  na cewa  sabon ƙudiurinsa na bada ilimi kyauta  zai sa dubban yara a dawo dasu makaranta  domin samun ingantaccen ilimi, ya kuma ƙara da cewa dole ne a kawo karshen barace barace wanda ko addini bai amince da  wulakanta kai ba da sunan bara.

Anasa jawabin Alasan Ado Doguwa yace  sun ziyarci gwamanan ne don nuna gamsuwarsa da kuma miƙa godiya ga gudunmawara da ya bayar don tabbatar dashi a matsayin shugaban masu rinjaye.

Leave a Reply

%d bloggers like this: