Gwamnatin jihar Kano ta yi sababbin nade nade a hukumomi mallakin Ta da kafafen yada labarai Dama hukumar jin dadin alhazai ta jihar.

Sanarwar ta fito daga babban daraktan yada labaran gwamnan jihar Kano mallam Abba Anwar yace gwamna Abdullahi Ganduje ya ja hankalin wadanda aka Nada mukaman wajan sauke nauyin da aka dora musu.

Wadanda aka nada a mukaman sun hadarda Lawan sabo a matsayin shugaban kamfanin buga jaridu naTriump da Ghali saddiq a matsayin shugaban gidan redion Kano da Hajiya Sa a Ibrahim data sake komowa a matsayin shugabar gidan talabijin na Abubakar Rimi (ARTV) da Mallam Abdullah Saleh Pakistan a matsayin shugaban hukumar alhazai ta jihar Kano sai Dr Aliyu Musa Aliyu a matsayin babban daraktan hukumar hisbah ta jihar Kano.

Leave a Reply

%d bloggers like this: