Ƙasar Uganda za ta fara yiwa shanu rigistar haihuwa don bunƙasa harkokin cinikayyarsu a faɗin ƙasashen duniya.

Ministan harkokin noma da kiwo na ƙasar Vincent Ssempijja ne ya bayyana hakan yayin buɗe wani aiki a ƙasar.
Ya ce yiwa shanun takarta da kuma lambobi zai haɓaka kasuwancin namansu da ma shanun masu rai waɗanda ake kaiwa zuwa ƙashashen waje.

Tun tuni wani ɓangare na ƙasashen ƙetare ya buƙaci sanin ingancin naman da suke siya da kuma sanin daga inda suke, wanda hakan ya sa suka ce ba za su ƙara siyan naman da bashi da rigista da gwamnatin ƙasar ba.
