Connect with us

Labaran ƙetare

Gwamnati za ta fara yiwa shanu takardar haihuwa

Published

on

Ƙasar Uganda za ta fara yiwa shanu rigistar haihuwa don bunƙasa harkokin cinikayyarsu a faɗin ƙasashen duniya.

Ministan harkokin noma da kiwo na ƙasar Vincent  Ssempijja ne ya bayyana hakan yayin buɗe wani aiki a ƙasar.

Ya ce yiwa shanun takarta da kuma lambobi zai haɓaka kasuwancin namansu da ma shanun masu rai waɗanda ake kaiwa zuwa ƙashashen waje.

Tun tuni wani ɓangare na ƙasashen ƙetare ya buƙaci sanin ingancin naman da suke siya da kuma sanin daga inda suke, wanda hakan ya sa suka ce ba za su ƙara siyan naman da bashi da rigista da gwamnatin ƙasar ba.

Click to comment

Leave a Reply

Labaran ƙetare

Amurka Da Saudiyya Sun Zargi Bangarorin Da Ke Rikici A Sudan Da Watsi Da Sulhu A Tsakaninsu

Published

on

Bayan sake sanya hannu kan yarjejeniyar dakatar da kai wa juna hare-hare a Sudan, an zargi bangarorin da ke rikici a kasar da sake yin watsi da batun sasanci a tsakaninsu.

Kasashen Amurka da Saudiyya, sun ce suna bincike kan bayanan da ke nuna cewa bangarorin kasar Sudan da ke yaki da juna, sun saba yarjejeniyar nan ta tsagaita wuta da suka cimma a baya-bayan nan.

Wannan na zuwa ne yayin da ake kokarin fara aikin samar da agajin jinkai gadan-gadan a Sudan.

Cikin wata sanarwa ta hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu da ke kai komon ganin an sasanta rikicin na Sudan, sun ce bangarorin ba su mutunta abin da aka amince da shi na cewa babu batun afka wa juna tun kafin yarjejeniyar ta fara aiki a ranar Litinin.

Kwamitin da ke sa ido kan tsagaita wutar dai, ya fada a jiya Talata cewa a binciken da ya gudanar ya gano yadda aka yi fatali da abun da aka tsaya a kai game da dakatar da kai wa juna hare-haren.

Ƙasar Sudan na fama da rikici tun bayan da aka smau sabani a tsakanin manyan sojojin ƙasar biyu.

Continue Reading

Labaran ƙetare

Kasar Saudiyya Ta Yankewa Wani Mutum Hukuncin Kisa Bisa Zargin Kai’wa Jami’an ‘Yan Sanda Hari

Published

on

An zartar wa da wani mutum hukuncin kisa a kasar Saudiyya ranar Talata saboda kai wa ’yan sanda hari.

Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida ta Saudiyya ta ce an yanke wa Anwar bin Jaafar bin Mahdi al-Alawi hukuncin kisa ne bayan samun sa da laifin bude wa wani ofishin ’yan sanda wuta.

Haka kuma an same shi da laifin bayar da mafaka ga wani wanda jami’an tsaro ke nema kan mallakar makami ba bisa ka’ida ba.

Sanarwar da Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida ta Saudiyya ta fitar ta kara da cewa kisa shi ne hukuncin duk wanda aka samu da irin wannan laifi.

Abaya hukumar ta sanar da cewa adaina kai hari wurare kamar yadda su ka sanar.

Continue Reading

Labaran ƙetare

Rikicin Sudan An Kaiwa Asibiti Da Wasu Bankuna Hare-hare A Birnin Khartoum Na Kasar

Published

on

An ci gaba da kai hare-hare Khartoum baban birnin ƙasar yayin da aka kai kari wani asibiti da wasu bankuna.

An kai hari bankunan da kuma asbiti tare da cigaba da lalata wurare muhimmai.

Dakarun RSF na ci gaba da kai hare-hare domin neman kwace iko da ƙasar.

Wani likita ya bayyanawa BBC cewar wasu mutane sun kutsa asibiti dauke da makamai a cikin dare.

Bangarori biyu ke faɗa a tsakani wanda a baya su ka yi kira da a tsagaita wuta domin samar da sulhu.

A halin yanzu bangare biyun na tattaunawar sulhu a birnin Jeddah na kasar Saudiyya.

A halin da ake ciki bangarorin biyu na ikirarin shirinsu na karɓar sulhu domin tsagaita wuta.

Tuni Najeriya ta ce ta kwaso ɗaliban ta da ke karatu a kasar bayan da rikicin ya ci gaba da tsananta.

 

 

 

Continue Reading

Talla

Trending

%d bloggers like this: