Ƙasar saudiyya ta shirya tsaf don raba Alƙu’ani mai tsarki ga maniyyata hajjin bana.
Mai kula da sashen wallafa litattatafai a ma aikatar addini da da’awa na ƙasar Sheƙ Abdulaziz Muhammad Alhamdad ne ya bayyana hakan, ya ce ma aikatar ta samar da hanyar koyar da aikin hajji da umara cikin sauti kuma an raba ga tashoshin jirgin sama da manyan wurare da mutane ke taruwa.
Haka kuma akwai litattafai da aka wallafa guda 52 cikin yare 30 na faɗin duniya don sauƙaƙa gudanarwa.