Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya sha alwashin inganta rayuwa da bunƙasa harkar kiwo musamman na fulani a jihar Kano.

Gwamna Ganduje ya samar da kwamitin da zai tsara hanyar da za  a samar da Ruga a jihar Kano.

Cikin wata sanarwa da haɗaɗɗiyar ƙungiyar Fulani ta Africa suka aike ga Gwamna Ganduje, ƙungiyar ta yaba matuƙa ganin yadda gwamnan ya sha alwashin samar da Ruga tare da kyautata rayuwa da kasuwancin Fulanin.

Babbab sakataren yaɗa labarai na gwamnan Kano Abba Anwar ya bayyana cikin wata sanarwar da ya fitar a yau cewa, Gwamna Ganduje ya buƙaci sauran gwamnnoni da su yi koyi da hakan ganin cewa al’umma na amfana da abubuwan da Fulanin ke samarwa kamar Nono da sauransu.

Ƙungiyar ta kuma buƙaci gwamnatin tarayya da ta yi koyi da matakin da gwamna Ganduje ya ɗauka.

Leave a Reply

%d bloggers like this: