A ranar Alhamis ce Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya yi kira ga hukumomin tsaro a Afrika musamman jami’an tsaro masu binciken sirri da su kara zage damtse a kan kwararar dukiyoyin haramun.

Shugaban kasa Ya Muhammad Buhari ya bayyana cewa yawan dukiyoyin haramun shi ke haifar da karuwar kalubalen tsaro da ake fuskanta daga masu cin riba daga irin wadannan dukiyoyin na haramun.
Buhari ya yi wannan jawabin ne a lokacin da yake bude taro na 16 na kwamitin jami’an tsaron sirri na Afrika (CISSA) a birnin tarayyar Abuja.

Jawabin ya fito ne da bakin mai taimaka wa Shugaban kasa Buhari na musamman kan yada labarai, Mista Femi Adesina,ya fitar cewa rashin zaman lafiya a nahiyar ta Afrika, yana faruwa ne sakamakon yawan dukiyoyin haramun a nahiyar wanda kimar su ya kai dalar Amurka bilyan 60 a duk shekara ya gurgunta su.

Shugaba Buhari ya kuma yi wa taron lakabi da, taken taron, “Hada-hadar dukiyoyin haram daga Afirka da kuma tasirinta ga tsaron kasa da ci gabanta.
Ya kuma bukaci masu ruwa da tsaki daga sassan hukumomin tsaron masu binciken sirri na kasashen Afrika 52 da su samar da wani hanya da zai samar da dubaru a kan yanda za a dakile duk wata dangantaka a tsakanin aikata laifi da zaman lafiya a nahiyar ta Afrika.