Wajibi ne shugaban kasa Muhammad Buhari ya tashi tsaye wajen kawo karshen matsalar tsaro da bangaranci a Najeriya,
Wannan jawabi ya fito ne ta bakin
Tsohon Babban Sakataren Kungiyar Kasashen Rainon Ingila, wato (Commonwealth), Emeka Anyaoku.

Anyaoku ya yi wannan jawabi ne a lokacin da ake kaddamar da wani littafi wanda Daddy Onyeama ya kaddamar a dakin taro na Yar adua dake Abuja.

“a cewar sa kafin kowace kasa mai tarin al’umma da kabilu daban-daban kamar Najeriya ta ci gaba, sai an bawa kowane bangare hakkinta, an gudanar da komai bai-daya, domin kishin ci gaban kasa, don habbakar kasa da Alummarta.

“Akwai batutuwa guda biyu a sha’anin ci gaban zaman tare a matsayin kasa daya al’umma daya. Na farko shi ne kowane bangaren al’umma ya san cewa kuma ya ji a jikin sa cewa an rungume shi ana tafiya tare. Wannan ke kara dankon zumunci da kaunar juna da kishi a tsakanin kowane bangare na al’ummar cikin kasa.
Saboda hakak Emeka Anyaoku yake bawa shugaban kasa muhammad buhari da ya tashi tsaye don magance matsalolin najeriya kafin wa’adin mulkinsa ya kare .

Leave a Reply

%d bloggers like this: