Gwamnan jihar kano Abdullahi Umar Ganduje tare da shugabannin Alummar Ibo mazauna kano sunyi Allah wadai da kalaman wasu shugannin Arewa na cewa Fulani makiyaya su baro kudancin kasar nan su dawo Arewa.
Shugabannin sun bayyana hakan ne a yayin wata liyafa da gwamnan ya shiryawa basaraken kan murnar Cikar su shekaru goma akan sarautar tasa.

Cikin wata sanarwa da sakataren yada labarai na gwamnan Kano Abba Anwar ya fitar Jim kadan bayan kammala liyafar a jiya lahadi.
Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje yace Najeriya kasa ce dake dauke da Dimbin Alumma ma banbanta addini da kabilu Wanda hakan ke nuna cewa dole a mutunta juna kasancewar Najeriya kasa ce guda daya.

Shima anasa jawabin sarkin Ibo anan jihar kano ya nuna damuwa game da kiraye kirayen ake wa fulani Makiyaya dasu dawo gida Arewa su bar Yankin Kudancin kasar nan, sar kin ya kuma yi Kira ga Alummar Ibo mazauna kano da su kasance masu bin doka da Oda.
