Wata Kungiya mai Rajin kare yancin Dan Adam tare da samar da daidaito a hukumomi da Ma’aikatun gwamnati SERAP ta Mika koke ga kotun hukunta manyan Laifuka ta duniya ICC inda take bukatar kotun tayi bincike da gano matsalar kin zuwa makaranta da yara ke you kasar nan da kuma yadda gwamnati ta gaza magance matsalar tsawon shekaru, Wanda hakan nada nasaba da cin zarafin yara da kuma take musu hakkokinsu na Dan Adam.
Kungiyar ta kuma bukaci babbar mai gabatar da kara ta kotun hukunta manyan Laifuka ta duniya da ta hukunta masu hannu cikin matsalar ciki kuwa har da Shugaban kasa mai ci a yanzu Muhammad Buhari.
Kungiyar ta kuma bukaci Mai gabatar da kara ta kotun Fatou BenSouda da tayi duk Mai yuwa don ganin an binciki lamarin.
Da kuma tsofaffin shugabannin kasar nan da suka gabata tun daga 1999 zuwa yanzu.
Takardar koken na dauke da sa hannun babbar mataimakiyar kungiyar Kolawole.

Leave a Reply

%d bloggers like this: