Anyi Kira da Malamai su kasance suna da kyakkawar Alaka tsakaninsu da dalibansu don samun ingantaccen ilimi.
Dr Ashir Tukur Inuwa ne ya bayyana hakan a wani taro da tsofaffin daliban jami’ar Bayero suka shirya don karramashi bisa samun shaidar digirin digir gir wato (Phd).
Ya kuma bayyana kyakkawar Alakar sa da Dalibansa shine ya janyo hankalin daliban shirya taron karramashi.
Dr ya kuma kara da cewa yaga daliban da ya koyar dasu Wasu ma tun daga Pramare gashi yanzu sun shirya taro don karramashi.
Daga karshe ya godewa daliban nasa da tare da farin ciki irin nuna mishi soyayya da suka yi tare da karramashi.
Dalibai ne daga sassa daban daban na jami’ar Bayero da na kwalejin Koyar da shari’ar ta Aminu Kano.
Taron ya kuma samu halartar fitattun yan jaridun jihar kano Ciki har da Abubkar Balarabe Kofar na’isa da ma sauransu.


