Har yanzu Al’ummar Najeriya na ci gaba da bayyana ra’ayinsu dangane da jerin sunayen da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika wa majalisar dattawan kasar, domin ta amince ya nada su a matsayin ministoci.
Idan ba’a manta ba a baya dai Shugaba Muhammadu Buhari ya ce zai yi kokari ya tabbatar ya nada mutanen da ya sani a matsayin ministocinsa.
A baya dai Shugaban ya bayyana cewa mafi yawan ministocin da ya yi aiki dasu a wa’adin mulkinsa na farko bai sansu sosai ba, Jam’iya ce ta bada sunayensu su.don haka
A halin yanzu dai Shugaba Buhari ya tura sunayen mutane 43, wanda a ciki an samu tsofaffin Ministocinsa 10 wadanda suka yi aiki da shi a wa’adinsa na farko, 33 sune sabbin sunaye sai dai akwai jerin sunayen Tsofaffin gwamnoni Wanda ake ganin suna da Laifuka a lokacinda da suke mulki a jihohinsu Wanda ake ganin in har aka tantance suka wuce to tamkar yakar cin hanci da rashawa bata sauya zani ba a Najeriya.
Sai dai wasu daga cikin ‘yan Najeriya sunyi korafin cewa akwai gyara saboda shakkunsu game da nagartar wadanda shugaban ke kokarin nadawa, musamman rashin ganin sunayen matasa sosai a cikin jerin sunayen ministocin da ya aike.
Wannan yasa Alumma suke ganin har yanzu bata canza zani ba a wa’adin mulkin Shugaban Buhari na biyu.


