Labaran ƙetare
An daure wata Mata yar Najeriya mai shekara 73 Saboda ta kashe Jariri A Amerika
Wata mata yar Asalin Najeriya mai shekaru 73 da take aikin Raino a kasar Amuraka, an yanke mata hukuncin daurin shekaru 15 a gidan yari sakamakon tayi sanadin mutuwar wata jaririyar da take Raino.
Dattijuwar mai suna Oluremi Adeleye ta yi sanadin mutuwar jaririyar ne sakamakon bata abincin da wuce ka’ida.
Inda aka gurfanar da ita gaban wata kotu mai suna Prince George dake Birnin Washington a Amurka.
Karkashin jagorancin Alkali Karen Mason inda ya ce Oluremi bata da wata hujja da za’a kareta kasancewar ta shayar da jaririyar ne A lokacin da jaririyar take a koshe.
Sai dai wacce ake Zargin ta nemi Afuwan iyayen jaririyar a gaban kotu inda tace bata yi hakan ne da niyar cutar da jaririyar bane tsautsayi ne.
Tuni Mai shari’a Karen Mason ya yankewa Oluremi Adeleye hukuncin daurin shekaru 15 a gidan yari.
Labaran ƙetare
Trump Ya Zabe Wanda Zai Masa Mataimaki
Dan takara shugaban kasar Amurka Donald Trump ya zabi Sanata J.D Vance a matsayin wanda zai masa mataimaki.
Sanata J.D Vance dai na da shekaru 39 a duniya wanda a baya ya kasance mai caccaka da sukar tsarin siyasar Donald Trump.
Sai dai daga baya ya dawo goya masa baya.
Donal Trump na takarar shugaban kasar Amurka ne karkashin jam’iyyar Republican.
A makon jiya ne aka kai hari Pennsylvania yayin da yake gangamin yakin neman zabe.
An bude wuta a wajen sai dai daga baya jami’an tsaro sun kubutar da shi duk da cewar ya ji rauni a fuskarsa da kunnensa.
Donal Trump ya ce an so a hallakashi ne a wajen taron amma Allah ya tseratar da shi.
Tuni shugaban Amurka Joe Biden ya yi Ala Wadai da lamarin.
Ya bukaci yan kasar da su hada kai don tabbatar da zaman lafiya.
Ana sa ran za a yi zaben ne a watan Nuwamban shekarar da mu ke ciki.
Labaran ƙetare
Ya Kamata A Dinga Jefe Ƴan Luwaɗi Da Maɗigo – Shugaban Ƙasar Burundi
Shugaban kasar Burundi, Evariste Ndayishimiye ya bayyana matakin da ya kamata a rinka dauka kan masu neman maza waɗanda aka fi sani da ‘yan luwadi.
Evariste ya ce kamata ya yi a rinka jefe su da su da masu auren jinsi inda ya ce hakan ba wani laifi ba ne.
Shugaban ya bayyana haka ne yayin ganawa da ‘yan jaridu a ranar Juma’a 29 ga watan Disamba.
Ya ce kasarsa ba ta bukatar duk wani taimako daga kasashen Yamma a kokarin kakaba musu sharadin luwadi da madigo.
Har ila yau, shugaban ya ja aya a cikin littafin Inijla inda ya ce Ubagiji ya haramta neman jinsi kwata-kwata.
Ndayashimiye ya kara da cewa kasarsa bata bukatar fara tattauna magana kan ‘yan luwadi da masu auren jinsi.
Ya ce luwadi da madigo hanya ce a bayyane tsakanin hanyar gaskiya ta ubangiji da kuma hanyar bata ta shaidan.
Burundi na daga cikin kasashen Afirka da suka haramta luwadi wanda hakan ya sa aka sanya hukuncin daurin shekaru biyu a gidan yari.
Labaran ƙetare
Shugaban Ƙasar Madagaska Andry Rajoelina Ya Lashe Zaɓe A Karo Na Biyu
Shugaban ƙasar Madagaska Andry Rajoelina ya sake lashe zaɓe karo na biyu, duk da kuwa ƙauracewa yin zaɓen da ƴan tsagin masu hamayya suka yi a yankin kudu maso Gabashin ƙasar ta tsuburin Afirka.
Andry ya samu kaso 58.95 cikin 100 na ƙuri’un da aka kaɗa, wanda hukumar zaben ƙasar ta sanar a yau Asabar.
Ƴan takarkarun tsagin hamayya Siteny Randrianasoloniaiko da Marc Ravalomanana sun samu kashi 14.4 da kuma kashi 12. 1 kowannensu.
Ƴan takarkarun tsagin hamayya su goma sun yi kira ga magoya bayansu da su ƙauracewa yin zaɓen, duk da kuwa an sanya sunayensu a jikin takardar ƙuri’ar zaben da aka riga aka buga.
Hukumar zaɓen ta ce kaso 46 cikin 100 sun fito kaɗa ƙuri’a, amman ba a ga fuskar ko ɗaya daga cikin ƴan takarkarun hamayya 12 a wajen sanar da sakamakon zaɓen ba ranar da safiyar yau Asabar.
Ƴan siyasar tsagin hamayyar sun zargi shugaba Rajoelina da ƙoƙarin cigaba da mulki ta hanyar da bata dace ba, sun zargi shugaban da bai’wa kotuna da jami’an hukumar zaben cin hanci.
-
Labarai8 months ago
Mafi Karancin Sadaki A Najeriya Ya Koma Dubu 99,241
-
Mu shaƙata2 years ago
Kun San Ma’anar Kalmar Chiza Dani? Waƙar Da Ke Tashe A Kwanakin Nan?
-
Labaran ƙetare5 years ago
Wajibi ne duk wani namiji ya Auri mata Biyar ko a ɗaure shi a gidan yari— Sarkin Swaziland
-
Al'ada5 years ago
Fahimta ta a kan matsalar aure a ƙasar Hausa
-
Labarai5 years ago
Ba kwaya ƴan sandan kano suka kama ba, babu sinadarin maye a cikin maganin – NAFDAC
-
Addini4 years ago
Lokutan da ake saurin karɓar addu’a
-
Lafiya6 years ago
Menene Genotype ? Amfanin yinsa kafin Aure – Mujallar Matashiya
-
Mata adon gari5 years ago
Sinadarin gyaran gashi – Adon Gari