‘Yansanda Sun Tarwatsa ‘Yanfashi a Garin Rano

A jiya Jumu’a rundunar ‘yansanda ta jihar Kano karkashin kwamishinan ‘yansanda na jihar CP. Ahmed Iliyasu ta samu rahoton cewa wasu ‘yan fashi hudu sun kutsa wani gida a garin rano dauke da makamai, nan take rundunar tayi dirar mikiya wanda hakan ya janyo ‘yan fashin suka tsere, jami’an ‘yan sanda kuma sukabi bayansu wanda har takai daya daga cikin ‘yan fashin ya rasa ransa yayinda uku daga ciki suka tsere zuwa cikin daji.

‘Yan sanda sun samu nasarar kwatar bindiga kirar gida, da kuma alburusai, tuni rundunar ‘yan sandan Kano ta baza komarta domin cafko sauran ‘yan fashin da suka tsere wanda bincike ya tabbatar da cewa suna daga cikin ‘yan fashin da suka addabi garin Rano, Bunkure, Kibiya, Tudun Wada da kuma dajin Falgore.

Akan hakan rundunar ‘yansanda ta jihar ke kara neman hadin kan sauran al’ummar Kano kan su cigaba da bata hadin kai da kuma sanar da ita kan duk wasu abu da basu gamsu dashi ba cikin gaggawa domin daukar matakin da ya dace.

Allah ya kara taimakon jami’an tsaronmu domin kare dukiya da rayukanmu.

Na samu sanarwa daga kakakin rundunar ‘yansanda ta jihar Kano DSP. Abdullahi Haruna Kiyawa.
27-06-2019.

Leave a Reply

%d bloggers like this: