Rundunar yan sandar jihar jigawa ta cafke wani matashi da ake zargin mahaukaci ne ya mai Suna Abdulkarim Mato bisa zargin sa da kashe wani yaro mai shekaru biyu da Fatanya.
SP Abdu Jinjiri shine kakakin yan sandan jihar Jigawa ya tabbatar da faruwar lamarin.
Inda ya ce yansandar karamar hukumar Miga sun samu Rahoto daga Dagacin kauyen Tsakuwa cewa wani mai Suna Abdulkarim Mato ya hallaka wani yaro tare da jikkata mutane Uku.
SP Jinjiri ya kara da cewa Wanda ake zargi ana alakantashi da tabin hankali, Yayi amfani da damar wajen kai farmaki a lokacin da iyayen yaran suke tsaka da ayyukansu a gonakinsu.