Kungiyar Kwadago ta Najeriya NLC ta koka matuka bisa yadda aka sake aike da sunan Chris Ngige a matsayin Minista,Wanda a baya ya kasance Ministan Kwadago da samar da aiki.

Sakataren Kungiyar Peter Ozo- Eson shine yayi wannan furucin inda ya bayyana cewa akwai Rikici a kasar nan Muddin Shugaban kasa Muhammad Buhari ya sake Nada Chris Ngige a matsayin Ministan Kwadago da samar da aiki a Najeriya.

Kungiyar ta bada shawarar da kada a nada a maida Ngige wannnan Ma’aikata a canza Masa saboda bashi da wani kyakkawar alaka tsakanin shi da kungiyar Kwadago, kuma bai San hakkin Alumma ba don haka bai dace da wannan kujera ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: