Labaran ƙetare
Wani Mutum mai dauke da cutar Ebola ya tsere Daga inda aka killacesu Ya shiga cikin Jama’a


Wani mutum da ke fama da cutar Ebola a jamhuriyar ta Congo ya tsere daga cibiyar lafiya inda yake karbar kulawa.
Mutumin da ba’bayyana sunanshi ba kamar Yadda Mujallar Alumma ta rawaito tace Ma’aikatar lafiya ta kasar ta tabbatar da faruwar lamarin inda ta bayyana hukumomi a kasar ta Congo. sun ce suna kyautata zaton mara lafiyar ya koma cikin jama’a.
Wanda lamarin zai iya haifar da gagarumar koma baya ga yunkurin kawo karshen cutar a kasar.
Hukumar lafiya ta duniya (WHO) dai tuni ta tabbatar da barkewar cutar Ebola a baya bayanan a kasar ta Congo a matsayin matsalar kiwon lafiya da ya shafi duniya baki daya.
Wannan dai shi ne barkewar cutar Ebola na biyu da ya fi kamari a kasar, inda izuwa yanzu an samu mutane kimanin 2500 da suka kamu da cutar a kasar ta Congo



Labaran ƙetare
Shugaban Ƙasar Madagaska Andry Rajoelina Ya Lashe Zaɓe A Karo Na Biyu


Shugaban ƙasar Madagaska Andry Rajoelina ya sake lashe zaɓe karo na biyu, duk da kuwa ƙauracewa yin zaɓen da ƴan tsagin masu hamayya suka yi a yankin kudu maso Gabashin ƙasar ta tsuburin Afirka.

Andry ya samu kaso 58.95 cikin 100 na ƙuri’un da aka kaɗa, wanda hukumar zaben ƙasar ta sanar a yau Asabar.
Ƴan takarkarun tsagin hamayya Siteny Randrianasoloniaiko da Marc Ravalomanana sun samu kashi 14.4 da kuma kashi 12. 1 kowannensu.

Ƴan takarkarun tsagin hamayya su goma sun yi kira ga magoya bayansu da su ƙauracewa yin zaɓen, duk da kuwa an sanya sunayensu a jikin takardar ƙuri’ar zaben da aka riga aka buga.

Hukumar zaɓen ta ce kaso 46 cikin 100 sun fito kaɗa ƙuri’a, amman ba a ga fuskar ko ɗaya daga cikin ƴan takarkarun hamayya 12 a wajen sanar da sakamakon zaɓen ba ranar da safiyar yau Asabar.

Ƴan siyasar tsagin hamayyar sun zargi shugaba Rajoelina da ƙoƙarin cigaba da mulki ta hanyar da bata dace ba, sun zargi shugaban da bai’wa kotuna da jami’an hukumar zaben cin hanci.
Labaran ƙetare
Isra’ila Ta Amince Da Tsagaita Wuta Na Tsawon Awanni Huɗu Kullum A Arewacin Gaza


Ƙasar Isra’ila ta amince a tsagaita wuta na awanni huɗu a kullum a arewacin Gaza, don a bai’wa fararen hula damar ficewa daga yankin.

Fadar gwamnatin Amurka ce ta sanar da hakan a yau Alhamis, duk da cewa shugaban ƙasar Joe Biden ya ce babu cikakkiyar tsagaita wuta.
Biden ya yabawa Fara-ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu bisa ɗan dogon hutu a faɗan, bayan tsawon wata daya da aka ɗauka ana fafata rikicin.

Sojojin Hamas da Isra’ila yanzu kowanne yana maɓoyarsa, kusa da inda ake gwabza faɗan a birnin Gaza, a yankin arewacin Zirin Gaza.

Mai magana da yawun sashin tsaron ƙasar John Kirby ya sanar da manema labarai cewa, Isra’ila za ta fara Ƙaddamar da Dakatar da faɗan na awanni huɗu a kullum a yankin na Arewacin na Gaza.

“Isra’ilawa sun sanar da mu cewa, ba za a samu aikin sojin su a yankin ba na tsawon lokutan da aka ɗauka, kuma hakan zai fara daga yau.”
Labaran ƙetare
An Sake Cafke Tsohon Shugaban Ƙasar Gini Bayan Ya Tsere Daga Gidan Yari


An sake cafke tsohon shugaban gwamnatin soji ta ƙasar Gini Moussa Dadis Camara a jiya Asabar, bayan ya tsere daga babban gidan yari a Conakry babban birnin ƙasar.

Shugaban sojojin ƙasar ta Gini Ibrahima Sory Bangoura ya tabbatar da hakan, ya kuma ce Camara yana cikin ƙoshin lafiya, kuma an mayar da shi gidan yarin na Conakry.
Ya kuma ce an kuma cafke mutane biyu da suka tsere tare da shi, wato Moussa Tiegboro Camara da Blaise Gomou. Kuma an mayar da su gidan yarin su ma.

Sannan sojojin sun bayyana cewa, ana ta ƙoƙari don ganin an kamo ragowar ɗayan da suka tsere tare, wato Claude Pivi.

Kotun ɗaukaka ƙara a ƙasar wacce ta ke a Conakry, ta bayar da umarnin a yi cajin su da babban laifi dukka su huɗun.

Moussa Camara dai ya Ƙaddamar da juyin mulki a ƙasar, ranar 23 ga watan Disambar shekerar 2008. Wanda kuma ya zama shugaban gwamnatin sojojin ƙasar.
-
Mu shaƙata10 months ago
Kun San Ma’anar Kalmar Chiza Dani? Waƙar Da Ke Tashe A Kwanakin Nan?
-
Al'ada5 years ago
Fahimta ta a kan matsalar aure a ƙasar Hausa
-
Labaran ƙetare5 years ago
Wajibi ne duk wani namiji ya Auri mata Biyar ko a ɗaure shi a gidan yari— Sarkin Swaziland
-
Labarai5 years ago
Ba kwaya ƴan sandan kano suka kama ba, babu sinadarin maye a cikin maganin – NAFDAC
-
Addini3 years ago
Lokutan da ake saurin karɓar addu’a
-
Bidiyo3 years ago
Wanene Halilu Ahmad Getso? Ƴar cikin Gida
-
Lafiya5 years ago
Menene Genotype ? Amfanin yinsa kafin Aure – Mujallar Matashiya
-
Labarai8 months ago
Akwai Jihohi Goma Da Zaɓen Gwamna Bai Kammala Ba A Najeriya Ko Har Da Kano?