A yau Asabar ne Jami’an tsaron Farin Kaya wato DSS suka je gidan mawallafin jaridar Sahara Reporters da ke yada labaranta a Shafukan yanar gizo gizo, mai Suna Sowore Omoyele.
Sowore ya kasance da takaran shugaban kasa a jam’iyar ACC, a zaben 2019
Rahotanni na nuni da cewa kama mawallafin na da alaka da kiraye-kirayen da akaji yana yi kwanan nan na Neman a yi wa gwamnatin shugaban kasa muhammad Buhari juyin mulki la’akari da yadda tafiyar gwamnatin tasa take na gaza gamsar da Jama’ar Najeriya.
Kafin a cafke shi dai Omoyele Sowore, na shirin jagorantar zanga zangar neman juyin mulki a Najeriya wanda ya bayyana cewa zata gudana a ranar Litinin 5 ga wannan watan na Agustan da muke ciki.
Madogara liberty