Wani babban malami da ya shafe fiye da shekaru 40 yana koyarwa a makarantar Allo ya bayyanawa mujallar Matashiya cewa, suna farim ciki da gyara karatun almajiranci da gwamnati ke ƙoƙarin yi a jihar Kano.

Mallam Khalidu Tudun Murtala ya ce ba a son ransu suke barin almajirai na yawo kwararo kwararo don yin bara ba kuma idan gwamnatin ta shogo don tallafawa za su yi farin ciki da hakan.
Mallam Khalidu ya ce da yawan mutane na tunanin gwamnati na tallafawa almajirai alhalin babu wata hanya da almajiran ke morar gwamnatin duk da kasancewarsu ƴan ƙasar Najeriya kuma suna da haƙƙi a kan gwamnati.

