Hukumar Hisbah a jihar Kano tayi kai sumame Wasu unguwanni a jihar Kano inda tayi nasarar kama Wasu mata da matasa da suke zargin su day yawace yawace suna gudanar da badala.

Mukaddashin Kwamandan hukumar ta hisba Malam Shehu Tasi’u ya nuna kyama da kan yadda ake yin badala a Wasu unguwanni da sukayi kyaurin suna a jihar Kano.
Inda yace suna nan zasu cigaba da kai sumame unguwanni da ake gudanar da badala.

Cikin Unguwannin da aka kai sumamen inda akayi nasarar cafke a matasa maza da mata a unguwannin Gidan Zoo da Gwazaye.

