Shugaban kasa Muhammad Buhar ya godewa miliyoyin Yan Najeriya bisa watsi da sukayi da kiraye kirayen da Wasu bata gari suka rika a yadawa a kafafen sada zumunta na fitowa zanga- Zangar juyin juya hali.

Jawabin godiyar ya fito ne ta Bakin babban mai taimaka masa kan kafafen yada labarai Malam Garba Shehu.

Inda ya bayyana cewa Shugaban yayi godiya matuka game da yadda Al’ummar kasar nan suke bashi goyon baya ba don gwamnatinsa ba sai don cigaban Kasa baki daya.

Haka zalika Shugaban kasa Muhammad Buhari yayi Kira da Mutanen da suke kiraye kirayen zanga zanga da nufin tayar da hankulan Al’umma da su canza tunani kan haka.

Leave a Reply

%d bloggers like this: