Connect with us

Labarai

Sojoji sun kashe ƴan sanda uku tare da kuɓutar da masu garkuwa da mutane – Inji Ƴan sanda

Published

on

Rundunar ‘yan sanda ta Najeriya ta zargi wasu sojojin kasar da hallaka jami’anta uku tare da raunata wasu bayan da sojojin suka bude wa wata tawagar ‘yan sandan wuta a jihar Taraba.

Lamarin ya faru ne a kan hanyar Ibi zuwa Jalingo, kamar yanda wata sanarwa da ‘yan sandan suka fitar ta bayyana cewa tawagar ta masu kai daukin gaggawa ce ta Intelligence Response Team (IRT).

Sanarwar ta ce tawagar tana karkashin jagorancin Felix Adolije, mataimakin sufuritanda na ‘yansanda, inda ta je jihar domin kama wani da ake kira Alhaji Hamisu, wanda ake zargi da cewa kasurgumin mai satar mutane ne.

Daga nan ne sai kawai wasu “sojoji na Najeriyar suka bude wa tawagar wuta ba kakkautawa, lamarin da ya sa sojojin suka kubutar da wanda ake zargin inda ya tsere har yanzu ba a san inda yake ba, a cewar kakakin ‘yan sandan na kasa, Frank Mba.

Amma kakakin sojin Kanar Sagir Musa ya musanta zargin na ‘yan sanda, yana mai cewa sun yi ba-ta-kashi ne da masu satar mutane.

Sanarwar ‘yan sandan ta kara da cewa jami’an ‘yan sandan sun kama mutumin ne za su kai shi hedikwatar ‘yan sanda ta jihar a Jalingo lokacin da sojojin suka bude musu wuta, duk kuwa da cikakkiyar shedar da ke nuna cewa suna kan aikinsu.

Bayan ‘yan sandan, lamarin ya kuma rutsa da ran wani farar hula, da sufeto da kuma wasu ‘yan sandan biyu masu mukamin saja, yayin da wasu ‘yan sandan kuma da ba a bayyana yawansu ba suka samu raunuka.

Sai dai rundunar sojin ta bakin mai magana da yawunta kanar Sagir Musa, ta musanta zargin, tana mai cewa ta yi tsammanin ‘yan sandan tawaga ce ta masu satar mutane domin wasu mutane ne daga yankin sun nemi ta kai musu dauki saboda masu satar jama’a sun kai musu hari.

A dalilin haka ne suka “tsayar da mutanen da ke tafiya a wata motar Bas amma suka ki tsayawa, dalilin da ya sa suka bude musu wuta domin kubutar da mutanen da ake zargin an sace”.

“Sai daga baya ne daya daga cikin wadanda suka tsira ya shaida mana cewa su ‘yan sanda ne daga Abuja, kuma an turo su ne domin gudanar da wani aiki na musamman kan masu satar mutane”.

Sojojin sun ce ‘yan sandan ba su sanar da su cewa za su gudanar da wannan aiki ba, kuma rundunar ‘yan sandan ta jihar Taraba ta ce ba ta san da zuwansu ba.

‘Yan sandan suna zargin mutumin, Alhaji Hamisu da kasancewa kasurgumin mai satar mutane, da suka dade suna nema saboda hannu a sace-sacen jama, ciki har na sace wani dan kasuwa mai harkar mai da aka yi kwanan nan a jihar ta Taraba.

Dan kasuwar mai sayar da mai wanda ba a bayyana sunansa ba a sanarwar, an ce sai da ya biya naira miliyan 100 aka sako shi.

Tuni aka tura wani mataimakin sufeto-janar na ‘yan sanda domin tsara yadda za a yi wa wadanda aka jikkata magani, yayin da kuma aka ajiye gawarwakin wadanda suka mutu a asibiti.

Shugaban rundunar ‘yan sanda ta kasa Muhammad Adamu ya bayar da umarnin gudanar da binciken gaggawa kan lamarin, in ji kakakin rundunar ta kasa Mista Frank Mba, mai mukamin mataimakin kwaminishinan ‘yan sanda.

Sai dai su ma sojoji ta bakin mai magana da yawunsu Kanar Sagir Musa ya ce suna kiran da a kafa kwamitin bincike na hadin gwiwa karkashin jagorancin ‘yan sandan domin tabbatar da gaskiyar abin da ya faru.

Ba dai wannan ne karo na farko da ake yin taho-mu-gama tsakanin ‘yan sanda da sojoji a Najeriya, lamarin da kan haifar da asarar rayuka.

#BBCHAUSA

Click to comment

Leave a Reply

Labarai

Ƴan Bindiga Sun Kashe Mafarauta 18 A Taraba

Published

on

Ƴan bindiga sun kashe mafarauta 18 a wani harin da suka kai a ƙaramar hukumar Bali da ke jihar Taraba.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa an kashe mafarautan 15 ne a wata arangama da ƴan bindiga a wani dutse kusa da garin Maihula a ranar Talata, 28 ga watan Nuwamba.

An ruwaito cewa ƴan bindigan da yawansu ya haura 200 sun yi yunƙurin kai hari a garin Bali Shalkwatar ƙaramar hukumar Bali, da wasu ƙauyukan da ke kewaye amma mafarautan sun yi artabu da su.

Ƴan bindigan waɗanda suke ɗauke da miyagun bindigu da suka fi na mafarautan, sun halaka mafarauta 15 a yayin artabun.

Wata mazaunin yankin mai suna Musa Umar ya bayyana cewa, mafarauta 14 ne suka mutu a wurin artabun, yayin da wasu mafarauta da dama suka samu raunuka, ɗaya kuma ya mutu a hanyar zuwa Asibitin Jalingo wanda adadin ya kai 15.

Shugaban kungiyar mafarauta na jihar Taraba, Adamu Dantala ya bayyana cewa an kashe mambobinsa 15 a wata arangama da ƴan bindiga.

Ya ce ƴan bindigan sun kuma yi wa mambobinsa kwanton ɓauna a kusa da garin Dakka a ƙaramar hukumar Bali inda suka kashe mafarauta uku.

 

Continue Reading

Labarai

Gwamnatin Tinubu Za Ta Inganta Tsaro Da Bunƙasa Tattalin Arziƙi – Fadar Shugaban Ƙasa

Published

on

A kasafin kudin shekara mai zuwa ta 2024, Bola Ahmed Tinubu ya ce babban abin da zai dage a kai shi ne tsaro da zaman lafiya a ƙasa Najeriya.

Fadar shugaban kasa ta ce shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sha alwashin samar da ayyukan yi tare da farfado da tattalin arzikin Najeriya.

A jawabin da ya gabatar, Bola Tinubu ya ce za a yiwa tsarin tsaro kwaskwarima a Najeriya domin a tsare rayuka da dukiyoyin jama’a.

Kundin kasafin kudin shekarar 2024 ya fi karkata zuwa ga wasu abubuwa takwas, kamar yadda mai magana da yawun shugaban ƙasa Ajuri Ngelale ya sanar a jiya Laraba.

Daga cikinsu akwai samar da hanyar da masu hannun jari za su kawo kudi domin yin kasuwanci wanda hakan zai inganta tattalin arziki.

Gwamnatin Tinubu za ta kara tsayawa tsayin-daka wajen yakar talauci da zarar an amince da kasafin kudin na 2024 a majalisun tarayya.

Kasafin kudin 2024 ya bada karfi a abin da ya shafi cigaban al’umma, musamman kananan yara wanda sai da su ake cigaba.

 

Continue Reading

Labarai

Ƴan Bindiga Sun Hallaka Manoma Mutane Biyu A Taraba

Published

on

Wasu da ake kyautata zaton ƴan bindiga ne sun kashe manoma biyu a gonakinsu a yankin Yangtu a jihar Taraba.

Kamar yadda Channels tv ta ruwaito, lamarin ya faru ne da sanyin safiyar ranar Talata a kudancin jihar da ke shiyyar Arewa maso Gabas.

Tsohon ɗan majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Ussa a majalisar dokokin Taraba, Habila Timothy, ya bayyana cewa manoman sun fito ne daga ƙauyen Kpambo.

Ya shaida wa gidan talabijin na Channels cewa manoman sun je gonarsu da ke Kwambai, garin da ya haɗa iyaka da ƙaramar hukumar da kuma yankin Yangtu.

A nasa ɓangaren, jami’in hulɗa da jama’a na rundunar yan sandan jihar Taraba, Abdullahi Usman, ya ce har yanzu rahoton bai kai ga ofishin ƴan sanda ba.

Ya kuma ƙara ba da tabbacin cewa hukumar ta ɗauki matakai kuma an yi nisa a kokarin kakkabe yan bindiga gaba ɗaya daga jihar.

 

Continue Reading

Talla

Trending

%d bloggers like this: