Hukumar Kula da zirga zirgar ababen hawa a jihar ano Karota sun sha alwashin magance matsalar cunkoso a yayin bikin babbar sallah.

Kakakin Hukumar Nabulusi Abubakar ne ya shaidawa mujallar Matashiya.

Ya ce a shirye suke don ganinan gudanar da bikin sallah ba tare da cunkoso ba, kuma sun ƙara jami ansu wuraren da ake iya samu cunkoso a jihar.

Sannan ya gargaɗi masu tuƙin ganganci da masu karya dokar titi da su yi kuka da kansu matuƙar suka yi arangama da juna.

Leave a Reply

%d bloggers like this: