Gwamnatin jihar Zamfara ta tuɓe sarkin Maru bayan da aka tabbatar da hannunsa cikin satar mutane da kashe kashe a jihar Zamfara.

Mai magana da yawun Gwamnan jihar Yusuf Idris Gusau, ya ce tsigewar ta kuma shafi dagacin garin Kanoma, Alhaji Lawal Ahmad wanda shi ma aka samu da laifin alaka da masu sata da garkuwa da jama’a.
Tun tuni dai ake ta zargin maau riƙe da sarautar gargajiya da hannu kan rikicin Zamfra da ya ƙi ci ya ƙi cinyewa.

Bayan zamansa gwamna a jihar Bello Matawalle ya tuɓe masu riƙe da sarautar gargajiya da dama waɗanda aka tabbatar da hannunsu kan rikicin.
